30 Satumba 2014 - 11:15
Palastinawa Sun Mayar Wa Netanyahu Da Martani Kan Kokarin Kare Kansa Da Yake Yi A Gaban UN

Jami'an gwamnatin kwarkwaryan cin gishin kai ta Palastinawa sun zargi Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Binjamin Netanyahu da yin wasa da hankulan al'ummomin duniya kan tabargazar da ya tafka a kan al'ummar Gaza.

Jami'an Palastinawa sun mayar wa Netanyahu da martani ne bayan da ya gabatar da wani jawabi a gaban babban taron majalisar dinkin duniya wanda ake gudanarwa a babban zauren majalisar da ke birnin New York, inda ya ce kungiyar Hamas daidai take da kungiyar ISIS, inda ya ce Hamas ta mamaye zirin Gaza, yayin da ISIS ta mamaye wasu yankunan Ayria da Iraki.

 

Daya daga cikin na hannun damar shugaban Palastinawa Mahmud Abbas wato Hanan Ashrawi ta bayyana cewa, Netanyahu yana kokarin wanke kansa ne dangane da kisan gillar da ya yi wa daruruwan mata da kananan yara a zirin gaza da sunan yaki da Hamas, wanda hakan ya kara zubar da mutuncin Isra'ila a idon al'ummomin duniya fiye da kowane lokaci a tarihinta. ABNA